✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace matar tsohon Gwamnan Bauchi

Ita ce matar tsohon Gwamnan soja na jihohin Bauchi da Osun, Kanal Theophilus Bamigboye (mai ritaya)

Matar tsohon Gwamnan mulkin soja a jihohin Bauchi da Ogun, Misis Jumoke Bamigboye ta kubuta daga hannun ’yan bindigar da suka sace ta ranar Asabar a yankin Oko Olowo na Karamar Hukumar Ilorin a Jihar Kwara.

Matar, wacce kuma Alkali ce a wata kotun majistare a jihar ta Kwara kuma mamba a kungiya kasa da kasa ta Rotary Club, an sace ta ne ranar Asabar a kan hanyarta ta dawowa daga gona bayan ta duba wani aiki.

Mijin nata, Kanal Theophilus Bamigboye (mai ritaya), ya tabbatar da lamarin a ranar Litinin gabanin sakin nata.

A cewar tsohon Gwamnan na mulki soja, “Tana kan hanyarta ta dawowa daga gona ranar Asabar da yamma, lokacin da ta ci karo da ’yan bindigar, wadanda suka yi mata kwanton bauna tare da tilasta mata fitowa daga motarta.

“Daga bisani sun tuntube mu a waya inda suka bukaci a biya su kudin fansa kafi su sake ta,” inji shi.

Kanal Theophilus ya ce suna ta kokarin ganin an kubutar da ita.

To sai dai da yake tabbatar da sakin nata ranar Talata, ya ce an sako ta ne bayan biyan wasu kudi da bai bayyana adadinsu ba.

“Sun sako ta a jiya [Litinin] da daddare, mun gode Allah, amma dai sai da muka biya kudin fansa, kuma yanzu haka tana asibiti tana samun kulawa.

To sai dai wasu majiyoyi da suka nemi a sakaya sunansu sun tsegunta wa Aminiya cewa da farko mutanen sun bukaci a ba su Naira miliyan 100 ne, kafin daga bisani a daidaita a Naira miliyan 50 a daren Litinin.

Kakakin ’yan sandan Kwara, SP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da sakin matar, inda ya ce sun kuma kama mutum uku da ake zargi da hannu a lamarin.

Sai dai bai ce komai ba a kan batun biyan kudin fansa.

%d bloggers like this: