✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace matan aure 4 da Yara 5 a Katsina

Mazajen matan sun tsere bayan 'yan bindigar sun kawo harin.

’Yan bindiga sun sace matan aure guda hudu tare da kananan yara biyar bayan sun kai hari a rukunin gidaje na Shema da ke Karamar Hukumar Dutsin-Ma ta Jihar Katsina.

Rahotanni sun ce, mazajen wadannan matan sun tsere daga gidajensu bayan sun fahimci kokarin ‘yan bindigar na kutsawa cikin gidajensu.

Aminiya ta rawaito cewa, ‘yan bindigar sun dirar wa gidajen ne da misalin karfe 11 da rabi na dare a jiya Lahadi kuma sun kwashe mintuna 30 suna cin karensu babu babbaka kafin isowar jami’an tsaro.

Daya daga cikin mazauna rukunin gidajen da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, a karon farko kenan da wadannan ‘yan bindigar ke kaddamar musu da hari.

Da yake tabbatar da sace mutum 9 da ‘yan bindigar suka yi, Mai Magana da Yawun rundunar ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya ce yanzu haka jami’ansu na bin sahu domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan makwanni da ‘yan bindigar suka kashe Kwamandan ‘yan sandan Dutsinma, ACP Aminu Umar.