✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace masu ibada 25 a cocin Katsina

An sace mutanen ne suna tsaka da ibada ranar Lahadi

Wasu ’yan bindiga da ba a gano su waye ba, sun sace masu ibada a 25 a wata majami’a da ke Karamar Hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Babban mashawarci na musamman kan harkokin Kiristoci ga Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari, Rabaran Ishaya Jurau ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an kai harin ne ranar Lahadi, lokacin da mutanen suke tsaka da ibada a cocin.

Rabaran Ishaya ya ce, “Cocin da suka kai wa hari a unguwar Jan-Tsauni take a Karamar Hukumar Kankara. Kuma sun sace mutane 25 suna tsaka da ibada.

“Sai dai ba su sace Faston cocin ba, amma sun raunata shi,” in ji Jurau.

Jaridar Thisday ta rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na safe.