✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun sace manoma 8 a kauyen Abuja

Sai dai har yanzu 'yan bindigar ba su tuntubi kowa ba

Wasu ‘yan bindiga sun sace wasu manoma su takwas a kauyen Mawogi da ke karamar hukumar Abaji a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Wani mazaunin Kauyen mai suna Aliyu Usman ya ce, lamarin ya faru ne a ranar Asabar da karfe 11:30 na dare.

Sannan ya ce ‘yan bindigar masu dauke da muggan makami sun shigo kauyen ne da yawa, inda suka kai hari kan wasu gidajen guda hudu tare da kwasar mazauna gidajen suka nufi cikin daji da suna harbe-harbe.

Aliyu ya ce, har yanzu ‘yan bindigar ba su tuntubi kowa ba tukunna.

Wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandar yankin Babban Birnin Tarayya, DSP Adeh Josephine ta hanyar aika mata sakon kar-ta-kwana, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba ta bayar da amsa ba.

A ‘yan watannin nan wasu kauyuka da ke karamar hukumar Abaji wadanda ke kan iyaka da jihar Neja suna fama da hare-haren ‘yan bindiga.