✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace mutum 100, sun sanya haraji a Neja

’Yan bindiga sun kashe mutum hudu tare da yin garkuwa da mutum fiye da 100 ciki har dakanan yara a Kananan Hukumomin Rafi da Mashegu…

’Yan bindiga sun kashe mutum hudu tare da yin garkuwa da mutum fiye da 100 ciki har dakanan yara a Kananan Hukumomin Rafi da Mashegu na Jihar Neja.

Daga cikin wadanda bata-garin suka kashe har da basaraken gargajiya da ’yan banga biyu da wani mutum daya a Karamar Hukumar Mashegu.

Maharan sun kuma sanya harajin Naira miliyan uku-uku domin dakatar da garkuwa da mutane a yankunan kananan hukumomin Rafi da Shiroro inda suka yi awon gaba da mutum 61.

Al’ummar yankunan Rafi da ’yan bindiga suka kai wa hari sun shiga yin kaura zuwa wasu wurare domin samun aminci.

Rahotanni sun bayyana cewa a mako uku da suka gabata mahara sun far wa kauyuka 14 a kananan hukumomin, inda suka sace yawancin mutanen a gonakin wake,  marasa da dawa.

Wani mazaunin yankin ya ce sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron kada a yi garkuwa da su, a yayin da ’yan bindiga ke sace masu amfanin gona.