Wasu gungun mahara da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi awon gaba da wani malamin Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya.
‘Yan bindigar wanda suka kai farmaki Unguwar Kuregu da ke yankin Wusasa a Zariya da misalin karfe 11 na daren ranar Litinin, sun yi ta harbe-harbe kan mai uwa da wabi.
- Ba ni da niyyar sake mayar da babban birnin Najeriya zuwa Legas idan na ci zabe – Tinubu
- APC za ta kaddamar da manhajar neman tallafin kudi daga ’yan Najeriya
Da ya ke tabbatar da faruwar al’amarin, Dagacin Wusasa, Injiniya Isiyaku Dallami Yusuf, ya ce gomman maharan sun kai farmakin ne sa’ilin da galibin jama’a ba su kwanta barci ba.
Ya ce maharan wadanda ke dauke da muggan makamai, in ban da taimakon jami’an tsaro da suka kawo dauki cikin gaggawa ba, da kila mutanen da za su dauka suna da yawa.
Dagacin ya kara da cewa, daga dukkan alamu ba malamin kwalejin kadai suka zo da niyyar dauka ba sakamakon yawansu da kuma irin makaman da suke dauke da su.
Ya yaba wa jami’an tsaro da suka tari hanzarin maharan a kan lokaci bayan kiran neman agaji da aka yi masu.
Wakilinmu ya kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, Muhammad Aliyu Jalige amma bai dauki wayarsa ba har zuwa lokacn hada wannan rahoto.