✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace makiyaya 6, sun nemi 16m a Kaduna

Maharan sun bukaci a biya su miliyan 16 kafin su saki makiyayan da suka sace.

’Yan bindiga sun jikkata mutum biyu tare da sace wasu makiyaya shida a wani garin Fulani da ke Laying-Jirgi kusa da garin Jere a Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.

Wani mazaunin garin, Labaran Saidu, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 11:23 na dare lokacin da ’yan bindiga suka mamaye garin.

Saidu ya ce “Wasu daga cikin ’yan bindigar sun zo ne a kan babura wasu kuma a kafa suka biyo ta cikin daji suka bude wuta kafin su tafi da wadanda abin ya shafa.”

Ya ce maharan daga baya sun kira waya, suka bukaci a biya su Naira miliyan 16 kafin su saki wadanda suka sacen.

Ya ce iyalan wadanda harin ya rutsa da su na tattaunawa da ’yan bindigar domin rage kudin fansar, kuma mutum biyu da suka jikkata suna wani asibiti da ke Jere.

Sakataren Masarautar Jere, Malami Zubairu Aliyu, ya tabbatar wa wakilinmu da harin, inda a cewarsa, “A yanzu da nake magana da kai, suna can a tsare saboda wadanda suka sace su na neman a biya su Naira miliyan 16.”