✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace mahaifiyar dan takarar Sanatan APC a Kano

’Yan bindigar sun sace mahaifiyar A.A Zaura da safiyar ranar Litinin.

’Yan bindiga ne sun sace mahaifiyar dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a Jam’iyyar APC, Abdulkarim Abdulsalam Zaura a Karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.

’Yan bindigar sun kai farmaki gidan dan takarar Sanatan na APC ne da sanyin safiyar Litinin, suka yi awon gaba da mahaifiyarsa, Hajiya Laure.

Shugaban Karamar Hukumar Ungogo, Injiniya Abdullah Garba Ramat, ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na Facebook.

“Innalillahi wa inna ilaihirraj’un, a yau mun tashi da mummunan labarin cewa a safiyar yau Litinin wasu ’yan bindiga sun yi wa Karamar Hukumar Ungogo dirar mikiya, inda suka yi awon gaba da mahaifiyar A.A Zaura zuwa wani waje da ba a sani ba. Allah Ka kubutar mana da Baba Laure.”

Cikakken bayani na tafe…