✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace ma’aikata a Jami’ar Abuja

’Yan bindigar sun yi awon gaba da ma’aikatan da ba a san adadinsu ba.

Wasu gungun mutane da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari Jami’ar Abuja inda suka yi awon gaba da wasu ma’aikatan jami’ar.

Wani mazauni, Dzarma Idris ya shaida wa Aminiya cewa, lamarin ya faru ne a cikin daren Talata da misalin karfe 12.14.

Dzarma Idris ya ce da zuwan maharan ne suke fara harbe-harbe kafin daga bisani su yi awon gaba da wani adadi na ma’aikatan jami’ar da kawo yanzu ba a iya tantancewa ba.

Wani mazauni da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce maharan da suka kwashe kimanin sa’o’i biyu suna cin karensu babu babbaka sun yi awon gaba da mutum bakwai.

Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan Sandan Abuja, Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ba ta yi wakilinmu wani karin bayani ba a kan hakan.

Kazalika, mahukunta jami’ar sun tabbatar da faruwar lamarin, sai dai duk sammakal domin kuwa ba su fayyace adadin mutanen da aka sace ba a jami’ar.

Sai dai kuma wasu bayanai na cewa, ’yan bindigar da suka kutsa kai rukunin gidajen Jami’ar da ke yankin Giri sun yi awon gaba da ma’aikata hudu da ’ya’yansu.