✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace limamin coci a Kudancin Kaduna

Sun yi wa gidansa dirar mikiya a cikin dare.

’Yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi awon gaba da wani limamin coci, Rabaran Fada Luka Benson, a gidansa da ke Anchuna da ke Masarautar Ikulu a Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna

Da yake shaida wa Aminiya abin da ya faru, wani mazaunin garin, Samuel Kukah, dan uwan Bishop Hassan Kukah, ya ce ’yan bindigar sun yi dirar mikiya ne a gidan Rabaran Luka da ke kusa da cocinsa na Katolika ne da misalin karfe 7:30 na dare, ranar Litinin, suka tafi da shi.

Duk wani yunkuri wakilinmu na jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, ya ci tura, domin har har muka kammala hada wannan lokacin wayarsa ba ta shiga.