✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace Kwamishina a Nasarawa

Lamarin na zuwa ne sa’o’i 48 bayan da wasu ’yan bindiga suka kashe wani malamin makaranta.

’Yan bindiga sun sace Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na Jihar Nasarawa, Yakubu Lawal.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar DSP Ramhan Nansel, ne ya tabbatar da sace da Kwamishinan a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Talata a Lafiya, babban birnin jihar.

Ya ce, tuni rundunar ta tura jami’anta da za su bi sahun ’yan bindigar da nufin ceto wanda abin ya shafa.

Aminiya ta gano cewa, ’yan bindigar sun sace Lawal ne a gidansa da ke garin Nasarawa Eggon a Karamar Hukumar Nasarawa Eggon ta jihar.

Lamarin, wanda ya faru a ranar Litinin, ya kara haifar da firgici a yankin da wasu ’yan bindiga suka kashe wani malamin makaranta a ranar Asabar.

An gano cewa ’yan bindigar sun kai farmaki gidan Kwamishinan ne da misalin karfe 8:45 na dare, inda suka fara harbi a iska, lamarin da ya tsorata mazauna yankin kafin su yi awon gaba da shi.

Haka kuma, wata majiya daga bangaren iyalinsa ta tabbatar wa wakilinmu cewa, an kwashe sama da minti 30 ’yan bindigar na harabar gidan kafin isowar jami’an tsaro..

Wakilinmu ya ruwaito cewa, lamarin na zuwa ne sa’o’i 48 bayan da wasu ’yan bindiga suka kashe wani malamin Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati (GSSS) a Karamar Hukumar Nasarawa Eggon, Auta Nasela da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar, yayin da wani malamin kuma ya samu raunuka.