✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace iyalan basarake a Taraba

'Yan bindigar sun yi awon gaba da matansa 2 da 'ya'ya shida.

’Yan bindiga sun sace mata biyu da ’ya’ya shida na Sarkin Mutumbiyu  Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.

Bayanan da Aminiya ta kalato sun nuna ’yan bindigar sun kai hari gidan basaraken mai daraja ta biyu da tsakar dare a ranar Alhamis.

Bayanai sun ce basaraken, Mai Shari’a Sani Muhammed (mai murabus), ba ya gidan nasa a lokacin da maharan suka kai farmakin.

Majiyarmu ta ce daga bisani maharan sun kira basaraken a kan ya tuntube su don tattauna yadda za a saki iyalan nasa.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

“An sace mata biyu da ’ya’ya shida na Dagacin Mutumbiyu da misalin karfe 1:00 na dare ranar Alhamis, kuma ana kokarin yadda za a kubutar da su,” in ji shi.