✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan bindiga sun sace daliban Islamiyya a Katsina

'Yan bindigar sun tisa keyar daliban yayin da suke tsaka da daukar karatu.

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da daliban wata makarantar Islamiyya a kauyen Sakkai na Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina.

Aminiya ta ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun sace daliban yayin da suke tsaka da daukar karatun yamma a harabar makarantar.

Ya zuwa yanzu babu wani cikakken bayani game da adadin mutane da aka sace a makarantar, amma wakilinmu ya rawaito cewar ‘yan bindigar sun yi awon gaba da dalibai takwas da malami daya.

Kazalika, ya zuwa wannan lokaci na hada wannan rahoto babu wani bayani kan inda aka boye daliban makarantar.

Har wa yau, a wani har da ‘yan bindiga suka kai Karamar Hukumar Batsari a Jihar, ya yi sanadin rasuwar mutum uku.

Wani mazaunin Batsari ya shaida wa wakilinmu cewar, gwaggonsa ta rasu sakamakon bugun zuciya da ta samu sanadiyar razanar da ta yi saboda harbin bindiga da ta ji.

Ya kara da cewa ragowar mutum biyun sun mutu sakamakon harbin harsashin da ‘yan bindigar suka yi.

“Lokacin da mahara suka shigo Batsari, mun fahimci cewar jami’an tsaro na kauyen Dankar wanda wasu ‘yan bindiga suka zagaye,” a cewarsa.

Sannan ya kara da cewar ‘yan bindigar sun sace mutum takwas a lokacin farmakin.

Ko da muka tuntubi kakakin ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce bai samu labarin faruwar wani hari daga ofishin ‘yan sanda na Batsari ba, sannan ya ce ba zai ce komai game da harin Faskari ba saboda dakarun soji ne ke kula da yankin.