✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda mahara suka sace daliban kwalejin lafiya a mahaifar Kwamishinan Tsaron Zamfara

’Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai mata a Kwalejin Kimiyyar Lafiya da ke Tsafe a Jihar Zamfara.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai mata a Kwalejin Kimiyyar Lafiya da ke Tsafe a Jihar Zamfara.

Maharan sun kutsa cikin dakin kwanan dalibai mata ne suka tisa keyarsu a kusa da harabar makarantar, kamar yadda wani malami a kwalejin ya tabbatar wa Aminiya.

Wani mazaunin garin, ya ce, “’Yan bindigar ba su yi harbi, kai-tsaye suka je suka balla kofar dakin kwanan daliban suka tafi da biyar daga cikinsu.

A takaice sai da gari ya waye wadanda da ke zaune a ginin da ke kallon na daliban suka san abin da ya faru saboda ba su yi harbi ba.”

Adamu ya ce bayan sun tafi da daliban, wata daga cikinsu ta kasa tafiya saboda tsabar tafiya da suka yi a kasa, shi ne suka dawo da ita.

Ya ce wadda ta kubutan ta bayyana cewa masu garkuwar sun shaid musu cewa kudin fansa suke so a biya a kansu.

Malamain kwalejin da muka zanta da shi, ya shaida mana a safiyar Laraba cewa baya ga daliban da aka sace, maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutane.

Kawo yanzu dai babu bayanin alkaluman daliban da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su a hukumance, duk da cewa wata majiya ta shaida mana cewa dalibai biyar ne aka dauke.

Wakilinm ya yi kokarin samun karin bayani daga Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, amma hakar ba ta cim ma ruwa ba.

’Yan bindiga sun hana Arewa sakat

Harin na zuwa ne mako guda bayan ’yan bindiga sun je gidan Kwamishinan Tsaro da Harkokin Jihar Zamfara, Ibrahim Mamman Tsafe, a garin suka kashe dansa.

Idan ba a manta ba a ranar Talata, Aminiya ta kawo rahoto inda Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gaggauta yin murabus saboda gazawarsa wajen magance matsalar rashin tsaro a yankin.

Ayyukan ’yan bindiga da ke garkuwa da mutane domin karbar kudaden fansa, gami da yi wa mata fyade da kuma kwacewa da lalata dukiyoyi ta hana al’ummar yankin Arewacin Najeriya rawar gaban hantsi.

Daruruwan dubban mutanen yankin sun yi kaura daga yankunansu a sakamakon ayyukan ’yan bindiga da suka tilasta daina ayyukan yau da kullum a wasu yankuna.

A lokuta da dama, miyagun kan sa wa al’ummomi haraji domin zuwa gona ko kauce wa hare-harensu.

Duk da kokarin da jami’an tsaro ke yi na magance matsalar, matsalar ta ki ci ta ki cinyewa, ko a baya-bayan nan, sai da ’yan bindiga suka yi amfani da bom suka kayar da wani jirgin kasa, suka sace akalla mutum 40, bayan sun kashe wasu, wasu kuma sun tsallake rijiya da baya.