Wasu ’yan bindiga da ake kyautata masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wasu dalibai a makarantar St. Albertine Seminary da ke Karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna.
Majiyar Aminiya ta ce, maharan na shiga kauyen Fayit, inda makarantar, wadda mallakin cocin Katolita ce take, suka fara harbe-harbe, kafin daga bisani su tafi da wasu daliban.
- NDLEA ta kama sarakuna suna shaye-shaye a Jigawa
- Ganduje ya sake korar tsohon Kwamishinan da ya yi ’murna’ da mutuwar Abba Kyari
“Ban san adadin daliban da aka sace ba, amma tabbas sun tafi da wasu. Sun shigo ne suna harbe-harbe, suka rikita mutanen wajen kafin su samu nasarar abin da ya kawo su,” inji majiyar da ta bukaci a sakaya sunanta.
Majiyar ta ce maharan sun yankin da ke Masarutar Fadan Kagoma ne da misalin karfe 10:00 na dare kafin wayewar garin Talata.
Sai dai kokarin Aminiya na jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ci tura domin bai dauki wayar wakilinmu ba yayin da ya kira, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.