’Yan bindiga sun kai hari tare da yin garkuwa da dalibai a makarantar sakandaren gwamnati (GSSS) da ke Kankara, Jihar Katsina.
Hakan ta faru ne a ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ya fara ziyarar mako guda a mahaifarsa ta Daura da ke jihar mai fama da rashin tsaro, musamman hare-haren ’yan bindiga masu satar mutane domin karbar kudin fansa.
- Yadda rashin tsaro ya sa ’yan Arewa dawowa daga rakiyar Buhari
- Rahama Sadau ce mace mafi tashe a Najeriya a 2020 —Google
A tsakar daren ranar Juma’a ne mahara dauke da muggan makamai suka yi wa makarantar kwanar dirar mikiya suka kuma yi awon da dalibai da ba a kai ga tantance yawansu ba.
“Sun iso Kankara ’yan mintoci bayan karfen 10 na dare a kan babura fiye da 100, wasunsu suka je wuce makarantar kai tsaye, sauran kuma suka tare hanyar zuwa makarantar daga garin Kankara domin hana a kai dauki”, inji majiyarmu.
Shaidu sun ce tun da yammacin ranar al’ummar yankin suka shiga cikin zullumi bayan sun lura da gilmawar mutane a kan babura dauke da makamai.
Majiyarmu ta ce sai da ’yan bindigar suka yi wa masu gadin makarantar ruwan wuta sannan suka tasa keyar daliban.
Daya ya yi batar dabo dayan kuma yana kwance a Babban Asibitin garin na Kankara ana jinyar sa.
Shaidu sun tabbatar wa Aminiya cewa: “Daga baya ’yan bindigar da suka tare hanyar sun yi musayar wuta da ’yan banga kafin ’yan sanda su mara wa ’yan bangar baya”.
Wani ganau ya ce wasu dalibai da suka tsere zuwa cikin jeji domin tsira da rayuwarsu sun dawo da safiyar Asabar, an kuma tsinci wasu daga cikin wadanda masu garkuwar suka tisa keyarsu a kan hanyar da ’yan bindigar suka ba.
Kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ’yan sandan da ke gadin makarantar sun yi dauki ba dadi da maharan wanda hakan ya ankarar da daliban.
“An harbi daya daga cikin jami’anmu kuma yana samun kulawa. DPO na Kankara da hadin gwiwar wasu caji ofis na aikin neman daliban da har yanzu ba a gani ba.
“Zuwa yanzu ba mu tantance yawan daliban da aka yi garkuwa da su ba, amma jami’anmu na ci gaba da aiki a kan lamarin”, a cewarsa.