✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace Dagaci da dansa a Bauchi

An sace Dagacin ne tare da dansa a daren Asabar

Wasu ’yan bindiga sun kai hari kauyen Zira da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, inda suka yi awon gaba da Dagacin garin mai suna Saleh Abubakar da dansa, Habibu Saleh.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Mohammed Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ’yan bindigar sun je kauyen da ke karkashin yankin Rishi da ke iyaka da Jihar Filato, da misalin karfe 2:00 na daren Asabar, inda suka yi garkuwa da mutanen.

Wakil ya ce tuni Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Umar Mamman Sanda, ya umurci baturen ‘yan sandan yankin (DPO) da ya ceto wanda aka sace ba tare da wani rauni ba.

“Tun daga nan ne rundunar ta aike da wata tawagar ’yan sanda, da sauran jami’an ’yan sanda domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, kuma a yanzu haka mutanenmu sun fantsama a daji suna neman wadanda aka sace, kuma muna tabbatar wa mazauna garin cewa nan ba da jimawa ba za a kubutar da su.”

Kakakin ya kuma ce Kwamishinan ya bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum tare da kai rahoton duk wani mutum da suka yi shakkar lamarinsa, domin suna yin duk mai yiwuwa don ceto wadanda lamarin ya shafa.

Hakimin yankin Lame, kuma Sarkin Yakin Bauchi Alhaji Aliyu Yakubu Lame shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce har yanzu wadanda suka sace su ba su tuntubi iyalansu ba.

Ya ce yanayin yana da ban tsoro idan mutane ba za su iya kwana da idanuwansu a rufe ba.

“Lokaci ya yi da Gwamnatin Tarayya za ta duba abin da ke faruwa a Arewacin Najeriya,” inji Hakimin.

Satar na baya-bayan nan dai na zuwa ne kwanaki biyar bayan ’yan bindigar sun kai hari garin Jamari sabuwa a Karamar Hukumar Alkaleri, inda suka kashe mutane hudu suka ji wa mutane uku rauni.