✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace basarake da matar aure a Kano

Lamarin ya faru a garin Bari na Karamar Hukumar Rogo ta Jihar

Wasu ’yan bindiga sun kai farmaki kauyen Bari da ke Karamar Hukumar Rogo ta Jihar Kano, inda suka sace wani basarake da wata matar aure.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren Talata a yankin.

Mutanen da aka sace su ne Shehu Bello Bari (Yariman Bari), sai kuma kanwa ga Dagacin garin na Bari, kuma matar aure mai suna Binta Abdulkadir.

Wani mazaunin kauyen, Suleiman Abdulqadir, ya shaida wa wakilinmu cewa ko kafin wannan harin, an taba sace dan uwan matar auren, kafin daga bisani a sake shi.

Ya ce, “Muna cikin matsananciyar damuwa da wannan harin gaskiya, saboda har yanzu babu wanda ya tuntubi iyalansu.”

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ba shi da masaniya a kan harin.