✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun sace basarake a Kaduna

Maharan sun yi awon gaba da shi a gidansa a daren ranar Laraba.

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Cif Joshua Ahmadu, Hakimin Chawai na Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna.

Mista Abel Adamu, shugaban kungiyar ci gaban Chawai (CDA) ne ya tabbatar da sace basaraken a ranar Laraba.

Adamu, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Raphael Joshua, jami’in hulda da jama’a na CDA, ya ce an yi garkuwa da basaraken gargajiya ne a daren ranar Talata.

Ya ce “wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba ne suka mamaye gidansa da ke Zambina.

“Mun samu bayanai cewa ’yan bindiga sun kai farmaki gidan basaraken da misalin karfe 9:30 na dare, kuma sun yi awon gaba da shi,” in ji Adamu.

Shugaban na CDA yana nuna rashin jin dadinsa kan lamarin tare da tabbatar wa mazauna yankin cewa za su yi iya bakin kokarin wajen ganin an sako shi cikin aminci.

“Tuni an sanar da hukumomin da abin ya shafa da kuma shugabannin jami’an tsaro da ke aiki a masarautar, kuma tuni suka fara kokarin ceto basaraken.

“Muna kira ga daukacin jama’a maza da mata na yankin Tsam da su yi addu’a don kubutar hakimin.”

Sanarwar ta kuma kalubalanci matasan masarautar da su rika kula da harkokin jama’a da muhimmanci domin kaucewa irin wannan ta’asa.

“Dole ne mu tsaya kan kafafunmu don tabbatar da cewa kasar nan ta zauna lafiya.

“Abin takaici ne cewa a wannan mawuyacin lokaci, matasa wadanda ya kamata su zama sun hada gwiwa don tabbatar da tsaro amma sun bige da shirme,” in ji shi.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa masarautar Tsam ta sha fama da sace-sace da hare-hare daga ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a baya-bayan nan.

Wasu daga cikin abubuwan da suka faru sun haifar da asarar rayuka yayin da kuma suka sha biyan makudan kudade don fansar wadanda aka sace.

Shugaban na CDA ya roki gwamnati da ta umarci hukumomin tsaro wajen tabbatar da cewa an ceto hakimin.

NAN ta samu labarin cewa jami’an rundunar ‘yan sandan yankin Kafanchan sun ziyarci iyalan wanda abin ya shafa tare da ba su tabbacin cewa a shirye suke su yi duk mai yiwuwa don ganin sun ceto shi.