’Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Basarake na masarautar Tal da ke Karamar Hukumar Panshik ta Jihar Filato a ranar Litinin.
Aminiya ta ruwaito cewa, da misalin karfe 1:00 na dare ne ’yan bindigar suka yi awon gaba da basaraken mai daraja ta uku, Ngolang Tal, Alhaji Dabo Gutus.
Wata majiya daga masarautar ta ce jama’a na ci gaba da kokarin tuntubar ’yan bindigar domin sanin inda aka kwana a kan lamarin.
Tuni dai Yarima Dakup Ezra kuma dan Majalisar Dokoki mai wakiltar Panshin ta Kudu, ya yi kira da a kwantar da hankula, yana mai jaddada cewa dawowar basaraken cikin aminci shi ne abin da suka sa a gaba a yanzu.
Ya yi kira ga al’ummar yankin da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda suka saba.
Ya bukaci da su guji aiwatar da wani lamari da zai kawo rikici a tsakanin al’umma tare da gargadinsu kan hatsarin da ke tattare da daukar doka a hannu.
Jami’in Hulda da Al’umma na Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, Alabo Alfred wanda ya tabbatar da sace basaraken, ya ce tuni bincike ya yi nisa kan lamarin.