’Yan Bindiga sun sace wata amarya da ƙwayenta huɗu a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.
Harin ya faru ne a ranar Asabar a garin Kwaren Gamba, kusa da Kuka Teke, wani ƙauye da yaran Bello Turji suka matsawa da hare-hare.
Shaidu sun ce ‘yan bindigar sun afka wa yankin sannan kuma tafi da waɗanda abin ya shafa, lamarin da ya jefa tsoro da tashin hankali a zukatan mazauna yankin.
Wani masani sha’anin tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana cewa al’ummar yankin na cikin matsananciyar damuwa.
Iyayen waɗanda aka sace suna cikin baƙin ciki, inda wani dattijo a yankin ya ce, “Al’amarin ya yi tsanani, kuma jama’armu sun shiga fargaba.”
Kwanaki kaɗan da suka wuce, ’yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 10 a jihar.
Sun kai hari ƙauyen Dantudu Lajinge, inda suka kashe mutum tara ciki har da ’yan sa-kai tare da sace matansu.
Wani mazaunin garin, Bello Dan-Tudu, ya ce, “Sun kashe su kamar dabbobi.”
Wani kuma ya ƙara da cewa maharan sun harbe mutum 10 a wuya, inda mutum ɗaya ne kaɗai ya tsira da ransa.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, Ayuba Hamisu, ya tabbatar da faruwar harin da kuma mutuwar mutanen da lamarin ya shafa.