✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace amarya a Neja

’Yan bindiga sun sace wata amarya ana tsaka da shagalin bikinta a kauyen Egbako da ke Karamar Hukumar Lavun ta Jihar Neja. Yakubu Mohammed, wani…

’Yan bindiga sun sace wata amarya ana tsaka da shagalin bikinta a kauyen Egbako da ke Karamar Hukumar Lavun ta Jihar Neja.

Yakubu Mohammed, wani dan uwan amaryar da aka sace, ya tabbatar wa da wakilinmu cewa ’yan bindigar sun yi awon gaba da mutane da dama.

Bayanai sun ce ’yan bindigar da suka kai harin na farko a ranar Asabar sun sake maimaita makamancinsa washe gari a ranar Lahadi, inda suka ci karensu babu babbaka a kusan yankuna 10 da ke garin Gbacitagi.

Sai dai bayan dawowarsu rahotanni sun bayyana cewa ba su riski kowa ba a sakamakon harin baya da suka kai wanda ya sanya mazauna suka tsere suka bar muhallansu.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun wawushe kayayyaki da kudaden da suka tarar a wajen bikin.

Aminiya ta ruwaito cewa, wasu ’yan bidinga sun kai hari kan wasu masu sallar jana’iza a kauyen Tsogi kamar yadda wani Danjuma Dabban ya shaida wa wakilinmu.

Maharan wanda aka ce adadinsu ya haura mutum 100 haye a kan babura akalla 40 sun farmaki kauyukan yankin ne dauke da muggan makamai ciki har da bindigogi kirar AK-47.

A cewar mazaunan garin, ’yan bidingar da suka yi kokarin kwasar shanu da kayan abinci masu yawan gaske yayin harin a garin Akare na Karamar Hukumar Wushishi, sun gamu da cikas a sakamakon karyewar wata gada da dole ita ce hanyarsu.

Hakan ne ya tilasta wa ’yan bindigar daukar wata hanya a yankin Sheshi Yissa amma ’yan sa-kai suka ci karfinsu.

Kwamishinan Kananan Hukumomi, Tsaron Cikin Gida, Ci gaban Al’umma da Al’amuran Masarautu, Emmanuel Umar ya tabbatar da faruwar hare-haren a Kananan Hukumomin Wushishi da Mashegu na jihar.