✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace abincin Kirsimeti a Kaduna

’Yan bindiga sun ƙwace wa wani magidanci kayan abincin da lemon kwalba da ya saya domin bikin Kirsimeti a yankin Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar…

’Yan bindiga sun ƙwace wa wani magidanci kayan abincin da lemon kwalba da ya saya domin bikin Kirsimeti a yankin Gidan Abe na Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.

Wani basaraken kauyen ya tabbatar wa wakilinmu cewa cewa a ranar Asabar ’yan ta’addan suka kai wa mutumin hari suka kwace kayan abincin Kirsimetin.

Ya bayyana cewa mutumin yana hanyar dawowa kauyen Gidan Abe daga sayo kayan buhun shinkafa da kayan miya da sauransu a Katari ne maharan da ke kan babura suka tare shi da bakin bindiga.

Basaraken ya bayyana cewa bayan ƙwace duk kayan abincin da mutumin ya sayi, sai maharan suka hau baburansu suka tsere da su, ba tare da sun sace mutumin ko sun illata shi ba.

Ya ce, “na samu bayani daga ƙauyen Katari inda na kai ziyara cewa ’yan bindiga a kan babur sun ƙwace wa wani mutum da ke ka babur kayan abinci a hanyarsa ta dawowa kauyen Gidan Abe domin bikin Kirsimeti.

Wakilinmu bai samu kakakin ’yan sanda na Jihar Kaduna ba, ASP Hassan Mansur, domin jin ta bakinsa game da wannan al’amari.