’Yan bindiga a jiya Laraba sun yi garkuwa da wani jami’in dan sanda a kusa da ƙauyen Kampani da ke Ƙaramar Hukumar Wase a Jihar Filato.
Lamarin dai a cewar majiyoyi daga yankin ya faru ne a lokacin da ɗan sandan da wani sojan ke kan hanyar zuwa unguwar Kampani bayan sun baro unguwar Zurak.
Ba zato ba tsammani jami’an tsaro biyu suka ci karo da ’yan bindigar da suka kai musu farmaki, inda suka yi nasarar sace ɗan sandan amma sojan ya tsere.
- An ƙayyade kuɗin tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin Kano
- EFCC ta tsare shugaban hukumar alhazzai ta kasa
Aminiya ta ruwaito cewa sojan da jami’in ɗan sandan suna aikin sintiri domin tabbatar da tsaro ne a unguwannin da ‘yan bindigar suka matsa da kai hare-hare da suka haɗa da Bangalala da Kampani da Zurak da sauransu a yankin.
Sahapi Sambo, shugaban matasa a yankin wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce “dukkansu biyun sun nufi Kampani ne wajen abokan aikinsu amma ’yan bindigar suka far musu a hanyar.
“Unguwannin da ke kewayen yankin na fama da hare-haren ’yan bindiga, lamarin da ya sa a kodayaushe jami’an tsaro ke sintiri don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
“Sai dai har ya zuwa yanzu, ba mu ji wani labari dangane da ɗan sandan ba,” inji Sambo.
Shugaban matasan ya ƙara da cewa, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da ‘yan sanda da ’yan banga na ci gaba da fadi-tashi domin ceto ɗan sandan da aka sace.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, bai waiwayi wakilinmu da ya nemi karin haske a kan lamarin ba.