✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun sa harajin N11m kafin girbi ga manoman Neja

’Yan bindigar sun kuma buƙaci babura da wayoyin salula da kayan abinci domin a sako mutanen da suka yi garkuwa da su.

’Yan bindiga sun saka harajin Naira miliyan 11 a ƙauyukan ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja kafin su ba su damar girbe amfanin gonakin su.

Manoman da harajin ya shafa da suka haɗa da: Dusai da Holobo da Sabon-Wuri da Hunyo da Meba da Farin-Ruwa da Kubashi da Mazame da Kakihun da Mai-kanwa da kuma Kuimo a Unguwar Gulbin Boka da ke gundumar Mohoro, sun shaida wa Aminiya cewa sun yi yunƙurin roƙon shiga tsakani, amma hukumomin jiha ko na tarayya ba su bayar da taimako ba.

Ɗaya daga cikin manoman da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun buƙaci babura da wayoyin salula da kayan abinci domin a sako mutanen da suka yi garkuwa da su.

Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja SP Wasiu Abiodun, ya ce zai yi ƙarin bayani, duk da cewa har zuwa lokacin da aka bayar da rahoton ba a samu ƙarin bayani ba.

Sai dai, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed (Mai ritaya), Kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Neja, ya tabbatar da cewa ana ƙoƙarin shawo kan lamarin cikin gaggawa.