Wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba dauke da makamai sun rushe ginin sabon ofishin diflomasiyyar Najeriya da ke Birnin Accra a kasar Ghana.
Mutanen dauke da manyan makamai da motar rushe gini sun rushe sabon ginin da ake yi na ofishin diflomasiyyar Najeriya da kuma masaukin manyan bakin Najeriya da ka kai ziyara kasar Ghana, a ranar Juma’a, 19 ga watan Yuni.
Majiyarmu ta ce wani babban attajiri ne a kasar ta Ghana ya yi korafin cewa ginin ofishin diflomasiyyar Najeriya ya shiga cikin filinsa, ya kuma kawo takardunsa da ke tabbatar da hakan, kafin daga baya ya dawo wajen tare da mutanen da suka rushe ginin.
Majiyar ta ce ofishin jakadancin Najeriya ya shaida wa ‘yan sandan kasar Ghana amma suka yi burus da su har aka rushe ginin.
Wasu shaidu sun ce ‘yan sandan Ghana sun isa wurin a daidai lokacin da ake rushe ginin inda suka yi ta gaisawa da masu rushe ginin.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto mahukunta a kasar ta Ghana ba su ce uffan ba a kan lamarin.
Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama a shafin sa na Twitter ya ce, “Mun yi tur da hare-hare biyun da aka kai wa ginin ofishin diflomasiyyarmu wadanda wasu da ba a san ko su waye ba suka yi da buldoza.
“Muna kan tattaunawa da gwmantin Ghana domin gano wadanda suka yi danyen aikin tare da ba wa ‘yan Najeriya da ke zaune a Ghana kariyar rayukansu da na duniyoyinsu”, inji shi.
Rahotanni sun bayyana cewa wadanda suka rushe ginin sun yi wa jami’an diflomasiyyar Najeriya da suka iske a wajen barazanar za su hallaka su idan suka kuskura suka yi masu magana.