’Yan bindigar da suka yi garkuwa da shugaban Karamar Hukumar Yagba ta yamma a Jihar Kogi, Mr. Pius Kolawole, sun bukaci a basu naira miliyan 100 a matsayin kudin fansarsa.
A makon da ya gabata ne ’yan bindigar suka yi awon gaba da Shugaban Karamar Hukumar yayin da suka harbe Kwamishinan Harkokin Fansho na Jihar, Solomon Adebayo da suke tare da shi.
- ‘Yan bindiga sun kashe mutum 17 a Benuwai
- An kama ’yan damfara masu kwaikwayon muryar aljanu a Katsina
Aminiya ta ruwaito daga wata majiya me tushe cewa, ’yan bindigar sun kira Sakataren Karamar hukumar da yammacin ranar Lahadi ce inda suka bukaci Iyalan shugaban karamar hukumar da su biya kudin fansarsa.
Duk da cewa sun yi alkawarin za su kira wayar da sanyin safiyar ranar Litinin don ci gaba da jin sharudan tattaunawar, sai dai bamu samu karin bayani ba kan yadda ta kasance.
Majiyar ta bayyana cewa, ’yan bindigar sun kuma tuntubi jagoran kungiyar shugabannin Kananan Hukumomin Jihar (ALGON) kuma shugaban Karamar Hukumar Ijumu, Mista Taofik Isah, kan bukatar ci gaba da tattaunawar.
Wakilinmu ya rawaito cewa, Iyalan shugaban karamar hukumar sun amince shugaban ALGON ya ci gaba da tattaunawar da ‘yan bindigar.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Asabar ce ’yan bindigar suka harbe Kwamishinan Harkokin Fansho na jihar Kogi, Mista Solomon Adebayo, yayin da suka yi awon gaba da Shugaban Karamar Hukumar Yagba ta Yamma, Pius Kolawole.
Duka su biyun dai an kai musu hari ne a garin Erukutu dake kan iyakar jihar da Kwara a yammacin ranar Asabar.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, ASP Williams Aya wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce kwamishinan ya riga mu gidan gaskiya ne bayan harsashin maharn ya same shi.