Kimanin mata dubu 22 ne ’yan bindiga suka yi wa mazajensu kisan gilla a Jihar Zamfara.
Kungiyar matasan Arewa ta AYF ce ta sanar da haka inda ta kara da cewa baya ga zawarawan, hare-haren ’yan bindigar ya mayar kananan yara dubu 44 marayu a jihar.
“Yana da wahala a yi kwana guda ba tare da an samu irin wannan aika-aikatar ba a yanzu”, inji Shugaban AYF, Gambo Ibrahim Gujungu.
Ya ce kimanin magidanta dubu 11 ne ’yan bindiga suka hallaka a cikin shekara takwas da jihar ta yi fama da matsalar ’yan fashin daji da sauran miyagu.
- Masari ya musanta ba wa ’yan bindiga toshiyar baki
- ‘Za a sake sanya dokar kulle a Najeriya’
- ’Yan bindigar da suka sace ’yan gida daya na neman miliyan N500
Gujungu ya nuna damuwa game da barnar ’yan bindiga da suka hada da kashe-kashe, satar dabbobi, fyade, garkuwa da kuma mutane a jihar da kuma yankin Arewa maso Yamma.
Ya bukaci a gaggauta daukar matakan magance matsalolin da ya ce na iya haifar da mummunan sakamako muddin aka ci gaba da zura ido ba tare da daukar matakan da suka dace ba.
Yankin Arewa maso Yamma wanda a can baya ya kasance mai zaman lafiya da aminci na fama da matsalolin tsaro da suka yi ajalin dubban mutane da tilasta wa wasu gudun hijira.
Baya ga irin asarar das matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa ta jawo, ta kuma jefa al’ummomi cikin fargaba musamman yankunan karkara inda manoma ba sa iya noma gonakinsu.