✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun mamaye garuruwa 64 a Filato — Gwamna Mutfwang

Da izinin Allah za mu yi nasara a kansu kuma mun kusa ganin ƙarshen waɗannan maƙiya,

Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro ta ƙara ƙamari, yana mai cewa a halin yanzu ’yan bindiga sun mamaye aƙalla garuruwa 64 na Jihar Filato.

A wata hirarsa da gidan talabijin na Channels a yau Laraba, Gwamna Mutfwang ya ɗora alhakin matsalar tsaron da ake fuskanta a jiharsa kacokam a kan ta’addancin ’yan bindiga da ke ƙara ta’azzara.

Gwamnan ya yi zargin cewa akwai masu ɗaukar nauyin hare-haren da ke aukuwa a jiharsa.

“A haƙiƙanin gaskiya babu wani bayani da zan yi face cewa akwai masu ɗaukar nauyin ta’addancin nan,” a cewar gwamnan.

“Abin tambayar shi ne, su wa ke ɗaukar nauyin ta’addancin? Wannan shi ne abin da hukumomin tsaro za su yi ƙoƙari su gano.

“Mun zo gaɓar da za a gano masu hannu a wannan lamari domin dole akwai masu ɗaukar nauyin waɗannan hare-haren.

“Waɗannan garuruwa da a bayan nan aka kai wa hari suna cikin yankunan da suka fuskanci hare-hare a 2023 amma suka sake gina alaƙaryar da kansu.

“Misali, a shekarar 2023 an kai wa ƙauyen Ruwi hari har aka kashe mutane 17, amma suka sake farfaɗowa suka gina matsugunninsu.

“Idan an ɗauki kusan shekaru 10 ana wannan hare-hare, shi yake nuna cewa akwai wasu da ke shirya wannan ta’addanci da gayya domin kawar da mutane daga doron ƙasa.

“A halin yanzu akwai aƙalla garuruwa 64 da ’yan bindiga suka mamaye a tsakanin ƙananan hukumomin Bokkos, Barkin Ladi, da Riyom na Jihar Filato.

“’Yan bindiga sun ƙwace iko waɗannan wurare sun sauya musu suna kuma mutane sun ci gaba da rayuwa a cikinsu.

“Sai dai ina fatan cewa nan da wani lokaci kaɗan hukumomin tsaro za su haɗa gwiwa domin kawo ƙarshen wannan matsalar.

Aminiya ta ruwaito cewa a makon jiya ne Gwamna Mutfwang ya yi iƙirarin cewa matsalar tsaron da ke addabar jihar ta wuce iya rikicin makiyaya da manoma.

“Dole ne na nanata cewa manufar waɗannan maƙiya ita ce tayar da hargitsi da hana zaman lafiya a jihar nan.

“Sai dai ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba har sai mun tabbatar da cewa burinsu bai cika ba.

“Masu tunanin cewa rikicin makiyaya da manoma ne ka haddasa matsalar tsaro su daina wannan tunani domin kuwa wasu ne ke sojan gona da zummar hana zaman lafiya a jihar.

“Ina mai tabbatar wa mutanen Filato cewa da izinin Allah za mu yi nasara a kansu kuma mun kusa ganin ƙarshen waɗannan maƙiya,” a cewar gwamnan.