✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kwace wasu sassan Katsina – Masari

Gwaman Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ce ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun kwace wasu sassan na Jihar Katsina. Gwamna Aminu…

Gwaman Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ce ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun kwace wasu sassan na Jihar Katsina.

Gwamna Aminu Masari ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba lokacin da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Muhammed Adamu ya ziyarci jihar, inda ya ce, “Wadannan’ yan bindiga suna kai farmaki a duk lokacin da suka ga dama, su kashe wadabda suka ga dama su kwace dukiyar wadanda suka ga dama su lalata dukiyar da suka ga dama.”

Gwamnan wanda Mataimakinsa Alhaji Mannir Yakubu ya wakilta ya shaida wa shugaban ’yan sandan cewa “A wasu sassan jihar masu garkuwa da mutane ba ma kawai suna kama mutanen da suke tafiya a kan hanyoyi ba ne, har cikin gida mutane suna kwance suke bin su.”  Ya kawo misali da abin da ya bayyana da “abin takaicin da ya faru da surukuwar Gwamnan wadda aka shiga har gidanta aka sace ta.”

Ya  ce shugaban ’yan sandan  ya zo ne a daidai wani lokaci na damuwa da firgici, inda ya ce Jihar Katsina ta tallafa kuma za ta ci gaba da tallafa wa shirin Farmakin Kasa da kudi da kayan aiki da muhalli, inda ya bayyana bayar da tallafin motoci aiki 12 ga ’yan  sandan.

Ya ce tuni gwamnati ta gana da shugabannin kananan hukumomi takwas da suka fi fama da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane don sanar da su cewa za a yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen ayyukan ta’asar ’yan bindigar da masu garkuwa da mutane a jihar.

Kananan hukumomi takwas su ne Jibiya da Batsari da Safana da Danmusa da Faskari da Sabuwa da Dandume da kuma Kankara, wadanda wasu daga ciki sun yi iyaka da Jihar Zamfara wadda take fama da hare-haren ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Tun farko Sufeto Janar Muhammed Adamu ya ce ya je jihar ce don duba kalubalen da tsaro yake ciki, musamman kan ayyukan masu garkuwa da mutane da ’yan  bindiga.

Ya ce, ’yan sanda suna bukatar samun bayanai game da ayyukan “wadannan miyagu.”

Ya ce, sababbin dabarun da ’yan  sanda suka dauka don yaki da masu garkuwa da mutane su ne na gano su da mamaye sansanoninsu.