✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta hana Gwamnatin Kano bincikar Ganduje

An ƙaddamar da kwamitocin shari’a guda biyu da suke gudanar da bincike kan almubazzaranci da dukiyar jama’a,

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin dakatar da kwamitocin bincike da gwamnatin jihar ta kafa domin binciken gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Idan ba a manta ba a watan da ya gabata ne gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da kwamitocin shari’a guda biyu da suke gudanar da bincike kan almubazzaranci da dukiyar jama’a, tashe-tashen hankulan siyasa da kuma bacewar mutane tsakanin shekarun 2015 zuwa 2023.

Duk a lokacin mulkin Ganduje, wanda yanzu shi ne shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.

Tuni dai kwamitocin karkashin mai shari’a Zuwaira Yusuf da Faruk Lawan suka fara zama.

A takardar da Ganduje ya gabatar, an jera shugabannin kwamitocin  da babban lauyan gwamnatin jihar, hukumar tattara kudaden shiga da hukumar kasafin kudi da kuma majalisar shari’a ta kasa (NJC) a matsayin wadanda ake kara.

Da yake bayar da wannan umarni, Mai shari’a S.A. Amobeda, ya hana gudanar da wani bincike, har sai an saurari karar da kuma yanke hukunci.

Alkalin ya kuma bayar da umarnin a gaggauta sauraren karar sannan daga bisani aka daga zaman zuwa ranar 28 ga watan Mayu da muke ciki.