✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajjin 2024: Za mu kammala jigilar mahajjata 10 ga Yuni —NAHCON

Jiragen biyu za su tashi a kowace rana a cikin kwanaki bayan ƙaddamar da jirgin mahajjatan a hankali zuwa tashi biyar a kowace rana,

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bayyana cewa za a kammala jigilar mahajjata da daga Najeriya zuwa kasar Saudiyya a ranar 10 ga watan Yuni ko kuma kafin hakan.

Mataimakiyar Daraktar Hulda da Jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta bayyana cewa jirgin farko zai fara jigilar maniyyata daga Jihar Kebbi ranar Laraba mai zuwa.

Ta kara da cewa daga baya jirage biyu za su rika tashi daga filayen jiragen sama 15 a kowace rana domin jigilar maniyyata 65,047 zuwa aikin Hajjin 2024 daga Najeriya.

“Ayarin jami’an farko da suka haɗa da ma’aikatan lafiya daga ƙungiyar likitoci ta kasa (NMT), ma’aikatan yaɗa labarai, masu kula da masauki, ’yan kwamitin ciyarwa da kuma tawagar masu karɓar baki sun tashi daga Najeriya a ranar Lahadi 12 ga wata domin tarbar maniyyatan.