✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu da Shettima za su fara biyan kudin ajiye abin hawa

Gwamnati na asarar sama da kashi 82 cikin 100 na kuɗaɗen shigar da ya kamata ta samu daga e-tags da ke bada damar shiga tashoshin…

Daga yanzu Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, za su rika biyan kudin ajiye ababen hawa a filayen jiragen saman ƙasar.

Hakan ya faru ne a bayan da Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da wata takarda daga Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta soke sassaucin harajin shiga ga duk wasu muhimman mutane da jami’an gwamnati masu amfani da filayen jiragen sama.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, wanda ya sanar da hakan ga ’yan jarida a ranar Talata, ya bayyana cewa gwamnati na asarar sama da kashi 82 cikin 100 na kuɗaɗen shigar da ya kamata ta samu daga sakamakon bayar da damar shiga tashoshin jiragen sama ba tare da biyan kudin ajiye abin hawa ba.

Ya bayyana cewa, tun farko takardar ta bada shawarar a keɓe shugaban ƙasa da mataimakinsa.

Amma Tinubu ya yi fatali da shawarar, inda ya nanata cewa shi da mataimakinsa tare da mataimakansu dole ne su biya kuɗaɗen shiga filayen jiragen.

Keyamo ya ce, shugaban ƙasa ya kore ni ya ce shi da Mataimakin Shugaban ƙasa za su biya, ya ce kowa zai biya.

Ministan ya koka da yadda manyan shugabanni da jami’an gwamnati da ke da kuɗin biyan haraji na kauce wa biyan kuɗaɗen, wanda hakan ya sa hukumomi suka dogara da ’yan kuɗaɗen da ake samu daga talakawa.