Dan Majalisar Wakilai mai Wakiltar Mazabar Gummi/Bukkuyum ta Jihar Zamfara, Sulaiman Abubakar Gumi, ya ce yanzu haka ’yan bindiga sun kwace fiye da kauyuka 30 na jihar.
Gumi ya ce a baya-bayan nan ’yan bindigar na kai hare-hare a kauyuka da dama na jihar, inda suka hallaka mutane 16 da raunata wasu da dama, tare da sace shanu da barnata dukiyoyin jama’a gami da cinna wa ofisoshin ’yan sanda da rumbunan abinci wuta.
- Zamfara 2023: Abubuwa 12 Da Suka Bambanta Dauda Lawal Da Sauran ’Yan Takarar Gwamna
- Shekararmu 5 Muna Fassara Alkur’ani zuwa Harshen Ibo —Kungiyar Musulmi Ibo
A cewarsa, sakamakon kai hari kullum da ’yan Bindigar ke yi, mutanen kauyuka fiye da 71 sun gudu, yayin da su ma manoma ke arcewa suna barin gonakinsu.
Dan Majalisar ya cewa samun sararin da ’yan bindingar suka yi ya sa sun dora wa mutane harajin ba gaira ba sabar, banda kudin fansa da suke karba idan sun sace wani nasu.
Dan Majalisar ya bayyana hakan ne yayin da yake bayani kan kudirinsa na neman tura karin jami’an soji yankunan da abin ya shafa, domin fatattakar ’yan ta’adda.
’Yan bindiga sun ba wa kauyukan Filato notis
Ya ce a halin da ake ciki ’yan Bindigar sun tura gargadi ga mazauna kauyukan Sabon Zama da Gindin Dutse da Anguwan Tsohon Soja da ta Yuhana da Mangu da ke Karamar Hukumar Wase a Jihar Filatu da su bar kauykansu ko su fuskanci hukunci daga garesu.
Yanzu haka dai mazauna kauyukan sun ce ’yan bindigar sanye da tsumman rufe fuska sun dira a kauyukan tare da ba su wa’adin kwana biyar su fice daga cikinsa, ko su shirya yaki da su.
Aminiya ta tattauna da wani mutum da ya tsere zuwa kauyen Pinau inda ya sanar da ita cewa ’yan bindigar sun yi barazanar kai musu hari idan har ba su bar kauyukansu ba, shi ya sa suka fara guduwa zuwa kauyen Pinau din da manyan birane.
To sai dai kakakin rundunar soji mai aikin tababtar da tsaro a Jihar Filato, Operation na Safe Haven, Manjo Ishaka Takwa, ya ce ba shi da labarin wannan gargadin da ake ikirarin ’yan bindigar sun aika wa kauyukan.