✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kone wani mutum kurmus a Katsina

Wannan hari daya ne daga cikin hudu da suka auku a makon nan.

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindiga a ranar Laraba sun kone wani mutum kurmus a cikin motarsa a Karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina.

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, wanda ke wakilcin mazabar Faskari, shi ne ya tabbatar da lamarin da cewa ’yan bindigar sun banka wa mutumin wuta da ransa.

Dan Majalisar ya ce akwai mutanen da ’yan bindigar suka kashe yayin da suka yi awo gaba da wasu da dama.

Da yake zantawa da wakilinmu, ya ce wannan hari daya ne daga cikin hare-hare hudu da suka auku cikin makon nan.

“Sun kai hari kauyen Kwakware inda suka yi awon gaba da mutum 17 kuma galibinsu mata ne.

“Bayan kwana daya da faruwar hakan ne kuma ’yan bindiga suka tare wani direba wanda suka kone shi kurmus a cikin motarsa.

“Ko a jiya Talata sai da suka kashe wasu mutum bakwai sannan suka yi awon gaba da mutum biyar.

“Abin takaicin shi ne yadda duk wuraren da wadannan hare-hare ba su da wata tazara mai nisa tsakaninsu da wani shingen binciken ababen hawa da dakarun soji suka kafa,” a cewarsa.

A kan haka ne mazauna suka tare babbar hanyar Funtua zuwa Sheme domin nuna fushinsu kan hare-haren ’yan bindiga da suka tsananta a yankunansu.

Duk wannan dai na zuwa ne bayan makonni biyu da aka yi ta tayar da jijiyoyin wuya biyo bayan kone wasu fasinjoji 38 da ’yan bindiga suka yi a Jihar Sakkwato.

A makon da muka yi bankwana da shi ne Gwamna Bello Masari na Jihar Katsna ya jagoranci tawagar wasu dattawa da suka kai wa Shugaba Muhammadu Buhari kokensu kan kashe-kashen mutane da ake yi a jihar.

Ko da suka kai wa Shugaba Buhari ziyarar ya ba su tabbacin cewa ana yin duk wata mai yiwuwa domin magance matsalar tsaro yankin Arewa maso Yamma da kuma sauran sassan kasar.