✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan bindiga sun kona wata dattijuwa da ranta

‘Yan bindiga sun kona wata kurmus bayan sun kai hari a gidan tsohon Daraktan Hukumar Tsaro ta DSS, Emeka Ngwu.

‘Yan bindiga sun kona wata kurmus bayan sun kai hari a gidan tsohon Daraktan Hukumar Tsaro ta DSS, Emeka Ngwu.

Mazauna sun ce ’yan bindigar sun cinna wa gidaje biyar wuta a kauyen Amagu Ihube da ke Karamar Hukumar Okigwe ta Jihar Imo.

Tsohon Daraktan na DSS, Emeka Ngwu, ya tabbatar da harin da kuma rasuwar dattijuwar a cikin gidan nasa.

Kawo yanzu dai babu tabbaci game da dangantakar Ngwu da dattijuwar da aka kashe.

Cikin gidajen da suka kone akwai gidan Kwamishinan Wasanni da Harkokin Matasa, Emeka Okoronkwo, da na tsohon Kwamishinan Yada Labaran jihar, Nnamdi Obiaraeri.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ASP Henry Okoye, ya tabbatar da harin, ya kuma ce sun fara bincike kan lamarin.

%d bloggers like this: