✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kona sansanin sojoji a Neja

Sun kona sansanin sojoji da ke makarantar sakandare a kauyen Allawa a Karamar Hukumar Shiroro

’Yan bindiga sun kona sansanin sojoji da ke wata makarantar sakandare  a kauyen Allawa a Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Shugaban Kungiyar Matasa Masu Kishin Yankin Shiroro, Abubakar Yusuf Kokki, ya shaida wa wakilinmu cewa da zuwan maharan sai suka wuce kai-tsaye zuwa makarantar da jami’an tsaron suka yi sansani.

“’Yan bindigar sun kai wa jami’an tsaron hadin gwiwa harin kwanton bauna inda aka yi dauki-ba-dadi a tsakaninsu.

“Maharan sun kona makarantar sakandaren Allawa, wato sansanin sojojin, suka fasa ma’ajiya suka kwashi makamai da kayan abinci, suka kuma tafi da motar jami’an tsaron daya”

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da adadin wadanda abin ya ritsa da su.

Abubakar ya ce, “Muna cikin babban hadari fiye da a koyaushe, kusan sai yadda wadannan bata-garin suka yi da mu.”

Ya ce, “Abin da ke faruwa na da matukar ban takaici,” al’ummomi da dama ’yan bindiga suka kai wa hari a ’yan kwanakin nan, suka kashe mutane, wasu da dama kuma suka yi kaura.

Kokarinmu na jin ta bakin kakakin ’yan sanda na Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, bai kai ga nasara ba.

Ba a samun wayarsa kuma mun tura masa ruutaccen sako, amma babu amsa, har muka kammala hada wannan rahoton.