Wasu ’yan bindiga sun far wa shingen tsaron jami’an tsaro da ke mil takwas na Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina, inda suka kona motocin jami’an tsaro guda uku.
Wata majiya ta sanar da mu cewa ’yan bindigar da suka kai kimanin su 50 sun fito ne daga unguwar Bugaje da ke yankin.
Sai dai majiyar ta ce wani mahayin babur ya sanar da ’yan sanda da ke aiki a shingen binciken zirga-zirgar ’yan bindigar kan aukuwar lamarin.
To sai dai a cewarsa, bayan sanar da su din ne wasu daga cikin sojojin suka tsaya a shingen tsawon minti 30, kafin daga bisani su bar wurin sun nufi Jibiya, bayan samun rahoton wasu ‘yan bindigar sun nufi garin daga Kauyen Tsambe.
“Motsin ’yan bindigar daga Bugaje sananne ne, hakan ne ya sa wasu sojoji suka nufi wajen domin far musu,” inji majiyar.
Kazalika, wata majiyar ta daban ta ce an samu musayar wuta da barayin dajin kafin su tsagaita wuta, inda suka ceci abin da za su iya suka kuma bar motocin na ’yan bindigar suka cinna wa wuta.
Kakakin Hukumar Hana Fasakwauri ta kasa, Isah Danbaba, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce babu wanda aka kashe ko aka raunata a musayar wutar.