✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kona motar yaki, sun kashe ’yan banga a Zamfara

Maharan sun sace mutane da dama bayan musayar wuta da sojoji a Dansadau.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga bakwai sannan suka kona motar yaki mallakar sojoji a garin Dansadau a Jihar Zamfara.

Gabanin fitowar alfijir din ranar Juma’a ’yan bindigar suka kai harin a garin da ke Karamar Hukumar Maru, suka kuma yi garkuwa da mutum 13 da suka hada da matan aure.

Shaidu sun ce tun da misalin karfe 3 na dare maharan suka rika kai hari a kauyukan yankin.

“Wadanda aka kashe sun hada da ’yan bangar da suka fito suka gwabza fada da ’yan bindigar. Bata-garin sun kona motar yaki da jami’an tsaro suka girke a yankin.

“Jami’an tsaro sun mayar da martarni amma da alama yawan maharan  ya fi karfinsu,” inij wani mazaunin garin Dansadau.

Har zuwa lokacin da muka kammala wannan rahoto ba mu samu jin ta bakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ba.

’Yan bindiga sun sha kai munanan hare-hare tare da kashe mutane da dama a garin na Dansadau mai nisan kilimita 100 daga Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Maharan sun tsananta kai farmaki a Dansadau ne bayan ’yan sa-kai sun yi wa wasu ’yan bindiga kisan gilla a watannin baya.

Mazauna garin sun kuma tare hanyar da wasu bata-garin ’yan kasuwa suke kai wa ’yan bindiga kayan abinci da sauran bukatu.

A kan haka ne su kuma suka hana al’ummar yankin zuwa gonakinsu, wanda ya sa da dama daga cikin manoma kasa girbe amfanin gonarsu.