✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe yaro a harin ofishin ‘yan sanda da INEC a Anambra

Sun lalata caji ofis da ofishin INEC a harin safiyar Laraba

’Yan bindiga sun kashe wani yaro yayin harin da suka kai kan ofinshin ’yan sanda da na Hukumar Zabe (INEC) ranar Laraba a Karamar Hukumar Idemili ta Kudu a Jihar Anambra.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga, ya ce yaron da ya cim ma ajali yayin harin, dan uwa yake ga wani  dan sanda a ofishin da ’yan bindigar suka kai wa hari.

Sanawar da ya fiar ta ce, “Sun farmaki ofishin INEC da na ’yan sanda da sauran gidajen da ke kusa.

“An kashe wani saurayi mai shekara 16, wanda dan uwa ne ga wani jami’i a oshin da akai kai wa harin.

“Batagarin sun zo da yawansu da misalin karfe 1:45am na yau, 1/2/2023 da motoci kirar Sienna guda hudu da bindigogi da fetur da sauran abubuwan fashewa,” in ji shi.

Majiyar ta ce bata-garin sun lalata ofishin INEC din ne ta hanyar jefa abun fashewa.

Lamarin da ya yi sanadiyar jikkata wata budurwa mai shekara 15 wadda aka dauke ta zuwa asibiti, in ji majiyar.

Kokarin da aka yi don jin ta bakin INEC game da harin, ya ci tura.