’Yan sintiri guda biyu sun mutu a wata musayar wuta tsakaninsu da ’yan bindiga a yankin Mutumbiyu na Karamar Hukumar Gassol ta Jihar Taraba.
’Yan bindigar sun raunata hudu daga cikin ’yan bangar da suka bi su domin kwato wata mata da maharan suka dauke suka tafi da ita cikin kungurmin jeji.
Byanan ’yan bindigar sun dauke matar ne ’yan bangar suka bi sawunsu har zuwa inda masu garkuwar suka daure ta da sarka.
Suna kokarin kwance matar ne ’yan bindigar da suka yi kwanto suka yi ta harbin su, nan take suka kashe biyu suka kuma raunata wasu hudu.
Shugaban ’yan sintirin ya umarci mutanen nasa da su janye bayan ya fahimci maharan sun fi su karfin makamai.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal ya ce ba shi da labarin abin da ya faru tukuna.