Akalla ’yan sanda tara ne suka rasu a wani hari da ’yan bindiga suka kai Kudancin kasar Habasha a safiyar Talata.
Babban jami’in dan sandan yankin shiyyar Bench-Sheko, Dawit Timotiwos, ya tabbatar da mutuwar ’yan sandan.
- Faransa ta sake kiran Benzema a karon farko bayan shekara 6
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina ya rasu
- ’Yan bindiga sun sace shanu 300 a Zamfara
- Injin jirgin Max Air ya lalace a sararin samaniya
Timotiwos, ya kara da cewa an samu karin jami’an ’yan sanda uku da suka ji rauni, amma bai bayyana ko su wane ne suka kai harin ba.
Sai dai ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bincike don gurfanar da wanda suka yi sanadin mutuwar jami’an.
Rikicin kabilanci a kudancin Habasha ya yi kamari kuma ya dade yana sanadin asarar daruruwan rayuka da muhallai.
Rikicin kabilancin ya sami asali ne daga neman madafun iko da kuma albarkatun kasa.