’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda biyar da farar hula uku a kauyen Gatikawa da ke Karamar Hukumar Kankara, Jihar Katsina.
Majiyarmu ta ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba da yamma bayan ’yan bindigar sama da 300 sun yi wa kauyen dirar mikiya suka firgita mazauna da harbe-harbe.
- An cafke matashi yana yi wa mahaukaciya fyade a Suleja
- Za a gina cibiyar dashen hanta a Kano, wadda babu irinta a Afirka ta Yamma
Bayanai sun nuna wasu daga cikin ’yan bindigar sun bi gida-gida suna kwace kudade da abinicin mutane, kana jama’a da dama sun ji rauni sakamakon harin.
Wannan harin ya jefa yankin cikin halin rashin tsaro wanda ya sa tuni wasu mazauna suka yi kaura zuwa kauyuka makwabta don tsira da rayuwarsu.
Wannan shi ne karo na biyu cikin wata guda inda ’yan bindiga suka kashe ’yan sanda.
A ranar 5 ga wannan wata, ’yan bindiga sun hallaka wani babban dan sanda, ACP Aminu Umar da wani takwaransa a yankin Dutsinma.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar wa wakilinmu da faruwan harin, inda ya ce daga Kano aka turo jami’an don aiki na musamman.