’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda hudu da wani farar hula a kamfanin tumatir na GBFoods Africa da ke kauyen Gafara a Karamar Hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, ya ce mutanen da suka samu raunin harbi a harin ba za su kirgu ba, domin ’yan bindiga kusan 500 ne suka yi wa kauyen da kamfanin kawanya, aka yi musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro.
- DAGA LARABA: Yadda Ake Gane Labaran Karya
- Har yanzu Manchester City ba tsarar Liverpool ba ce —Bernardo Silva
“’Yan bindiga akalla 500 ne suka kai hari kamfanin tumatir din da ke kauyen Wawu a Karamar Hukumar Ngaski, suka yi yunkurin sace shugabannin kamfanin.
“’Yan sanda hudu da wani mutumin kauyen sun rasa rayukansu sakamakon musayar wuta da aka yi a tsakaninsu da maharan,” inji shi.
A cewarsa, ’yan bindigar sun shiga kamfanin ne suna neman shugabannin kamfanin, sai dai an yi dauki-ba-dadi tsakaninsu da jami’an tsaro wanda a sanadiyar haka aka jikkata mutane da dama daga kowane bangare.
Ya ce wadanda suka ji rauni ba za su lissafu ba amma an kai wani asibiti wanda ba a bayyana sunansa ba ana ba su agajin gaggawa, yayin da su kuma ’yan bindigar suka kwashe gawarwakin ’yan uwansu.
Kakakin ya bayyana cewa an jibge karin ’yan sanda a yankin don tabbatar da komai ya daidaita.