Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami’anta guda hudu da kuma bacewar wani guda daya bayan ’yan bindiga sun kai musu hari a yankin Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
Hedikwatar ’Yan Sandan ta ce ’yan sandan sun gamu da ajalinsu ne ranar Juma’a a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua a lokacin da suke komawa Kano daga Minna.
- ’Yan Kasuwar Kantin Kwari 18 da aka sace sun isa gida
- Tsoron iyayenmu na hana maza neman aurenmu —’Yan matan barikin soja
- Ramadan: Ba ma bin ganin watan Saudiyya —Sarkin Musulmi
“Sauran 11 kuma, Kwamandansu ya jagornace su wurin gano gawarwaki da makaman wadanda suka kwanta dama, yayin da ake kokarin gano wanda ya bace din,” inji kakakin Rundunar, Frank Mba.
Sanarwar Frank Mba, ta hannun mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ta ce jami’an su 16 ’yan sandan kwantar da tarzoma ne da ke aiki a Jihar Kano.
Ya ce jami’an ’yan sandan na daga cikin rundunar Operation Puff Adder da aka tura Jihar Neja domin tabbatar da zaman lafiya daga matsalar tsaro ta ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ke addabar yankunan Jihar ta Neja.