✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 3 a Anambra

Rahotanni sun bayyana cewar an kai wa jami'an hari ne a kan hanyarsu ta zuwa Jihar Abia.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra, ta tabbatar da cewa wasu mahara sun kashe wasu ’yan sanda a ranar Juma’a a garin Ihiala da ke Karamar Hukumar Ihiala ta jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da DSP Tochukwu Ikenga, kakakin rundunar, ya fitar ranar Asabar a Awka.

Ikenga ya bayyana cewa, a ranar Juma’a da misalin karfe 2:40 na rana, ’yan sandan da ke aiki a yankin Ihaila, suka samu kiran gaggawa tare da kai dauki a hanyar Isheke, Ihaila, inda suka zakulo gawarwakin ’yan sanda uku tare da wasu da suka samu raunuka.

Kakakin ya ce, ’yan sandan da suka mutu suna tare da sashen kula da abubuwan fashewa (EOD) na rundunar ’yan sandan Jihar Delta.

A cewarsa, ’yan sandan uku suna kan hanyar zuwa Abia ne a lokacin da aka kai musu hari a yankin Ihiala.

Ya kuma ce a halin yanzu ana kokarin gano inda ’yan bindigar suka shiga.