Wasu ’yan ta’adda sun kashe akalla mutum 34 a wani sansanin ’yan gudun hijira da ke wata makarantar firamaren gwamnati a Karamar Hukumar Guma ta Jihar Binuwai.
Mai ba da shawara kan sha’anin tsaro na karamar hukumar, Christopher Waku, ya shaida wa Aminiya cewa wasu mutum sama da 40 kuma sun samu raunuka a harin da aka kai da misalin karfe 9 na dare ranar Juma’a.
- Masarautar Kano ta kara nada sabbin hakimai
- Yadda ’yan ta’adda suka sace yara da mata 100 a Ramadan a Zamfara
Da yake bayani kan abin da ya gani a wurin, Waku ya ce, “Mun gano gawarwaki 24 a cikin wani aji, da wasu 10 kuma a kan hanyar kauyen; su kuma an kashe su ne a yayin da suke kokarin tserewa.”
Kakakin ’yan sanda ta Jihar Binuwai, Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin rubutaccen sakon da ta tura wakiliyarmu cewa, “tabbas hakan ta faru.”
Wani shaida mai suna John ya bayyana mana cewa wata mata mai juna biyu da danta suna daga cikin ’yan gudun hijirar da ’yan ta’addan suka hallaka a harin.
Ya ce an kai harin ne a matsugunin ’yan gudun jiharar da ke makarantar firamaren da ke unguwar Mgban da ke yankin Nyiev a Karamar Hukumar Guma.
Ko a ranar Alhamis, Aminiya ta kawo rahoton kisan wasu mutum 46 da wasu ’yan bindiga suka yi a Karamar Hukumar Otukpo ta jihar ta Binuwai.
Mutanen da aka kashe, ciki har da iyalan shugaban karamar hukumar, Bako Eje, sun gamu da ajalinsu ne a yayin da ake zaman makokin wasu mutum uku da wasu mahara suka kashe kafin ranar.