Mahara sun bude wa mutum 13 ’yan gida daya wuta a yayin da suke barci da tsakar dare a gidansu da ke Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Kogi.
’Yan bindigar sun kuma harbe wani makwabcin ’yan gidan suka kuma raunata wasu masu yunkurin kai dauki bayan sun ji karar harbi a gidan mamatan.
Babban mai ba wa Gwamna Yahaya Bello Shawara Kan Tsaro, Isah Abdulkareem, ya tabbatar cewa da misalin 2.30 na daren Laraba 28 ga watan Yuli aka sanar da shi mummunan lamarin.
Ya ce tuni aka girke jami’an tsaro domin kare rayukan al’ummar yankin.
Ana yawan samun rikici tsakanin kabilun Ebirra da Bassa-Komu a karamar hukumar, wanda ya lakume rayuka da dama.
Sai dai daga bayan rikkcin ya lafa bayan gwamnati da hukumomin tsaro da sauran masu fada a ji sun shiga tsakani.
Kwamishinan Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi, Ede Ayuba, ya ce tuni suka fara bincike kan harin, da taimakon mutum daya da ya tsallake rijiya da baya daga cikin ’yan gidan.