✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga a kasuwa a Neja

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga biyar, wasu da dama kuma sun samu raunuka kasuwar Bassa.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga biyar, wasu da dama kuma sun samu raunuka a wani hari da suka kai wata kasuwa a Jihar Neja.

Bayan harin na Kasuwar Bassa, maharan sun kuma kai farmakin ne a wasu kauyuka na Karamar Hukuamr Shiroro ta Jihar.

“Kimanin ’yan banga biyar ne aka kashe a dauki ba dadin, an kuma lalata dukiya mai tarin yawa, yayin da mutane da dama kuma suna samu raunukan harbi, wasu kuma aka yi garuwa da su,” inji Shugaban Kungaiyra Matasa Masu Kishin Yankin Shiroro, Sani Abubakar Yusuf Kokki.

Ya ce sauran al’ummomin da aka kai fa harin sun hada da kauyukan Beri, Beri-Kago, Gatawi, Kini, Bmada da makwabtansu da ke yankin.

Sani ya koka da cewa hare-haren sun zama ruwan dare a kusa kowace rana a yankin.