✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe sojojin kamaru 6 a kan iyakar Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewar makiyayan sun kai harin ne a matsayin ramuwar gayya.

Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kai hari a kan iyakar Najeriya da Kamaru, inda suka hallaka sojojin Kamaru shida.

Wannan hari ya faru ne a yankin Akwaya da ke Kudu Maso Yammacin Kamaru.

Ɗan majalisar yankin ya bayyana cewa ɗaruruwan makiyaya ne suka kai harin kan wani sansanin soji a yankin, yayin da basaraken yankin ya ce maharan sun ƙone gidansa kurmus.

Rahotanni sun ce harin ramuwar gayya ne saboda kisan makiyaya da dama da sojojin Kamaru suka yi kwana guda kafin maharan su kai wannan farmaki.

A halin yanzu, yankuna da dama a Arewacin Najeriya na fama da hare-haren ’yan bindiga waɗanda suka addabi jama’a.

Waɗannan ‘yan ta’adda na kai hare-hare ƙauyuka, suna yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, tare da lalata dukiyoyin jama’a.

Mutanen karkara sun shiga tsaka mai wuya, yayin da hare-haren ya hana su gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali.

Suna kuma fuskantar matsalar barace-barace a birane, yayin da wasu ke rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Duk da ƙoƙarin jami’an tsaro, hare-haren ‘yan bindiga na ci gaba da yawaita a wannan yankin.